Hukumar Kula Da Yanayi Ta Kasa NIMET, ta yi hasashen samun hazo da kura kwanaki 3.
Sauyin yanayin zai fara daga ranar Litinin zuwa Laraba 9 zuwa 10 ga watan Disamba.
Hukumar ta fitar da sanarwar ce ranar Lahadi a Abuja.
Ta kuma ce, lamarin zai fi shafar arewacin kasar nan, arewa ta tsakiya inda nan ma za fuskanci kurar da kuma hazo
A Kudu ma za a yi hazo. Don haka sanarwar ta shawarci masu ababen hawa da su yi tuki cikin nutsuwa.
Ranar Talata za a sami hazo, sai Laraba inda nan ma hazon zai mamaye arewacin kasar nan, inji sanarwar.
Hukumar kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su lura da wannan gargadi, tare da yin aiki da hukumar domin kauce wa hadari.