
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai ɗimbin yawa da kuma iska mai ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar nan daga yau Litinin, 21 ga Yuli, zuwa Laraba, 23 ga Yuli, 2025.
A cikin wani sako da ta wallafa a shafin X (tsohon Twitter), NiMET ta bukaci jama’a da su dauki matakan kariya tare da yin taka-tsantsan da yiwuwar ambaliya da barnar da iska mai ƙarfi ka iya haddasawa a wadannan ranaku.
Hasashen hukumar ya nuna cewa a ranar Litinin za a samu ruwan sama daga rana zuwa yamma a jihohin yankin tsakiyar ƙasa kamar su Abuja da Niger da Filato da Nasarawa da Benue da kuma Kogi.
A ranar Talata, NiMET ta ce ana sa ran ruwan sama tun daga safe har zuwa tsakar rana a Abuja da Kwara da Nija da kuma Plateau.
A ranar Laraba da safe, ruwan sama da iska mai ƙarfi za su afkawa wasu sassan Arewa kamar Katsina, Kano da Bauchi da Sokoto da kuma Taraba, sannan daga baya kuma a Yobe da Jigawa da Kaduna da Borno da kuma Kebbi.