Hukumar kashe gobara ta Kano tace zata ɗauki ma’aikata sama da ɗari biyu tare da siyan sabbin motocin kashe gobara a shekara mai kamawa domin ci gaba da inganta ayyukanta a lungu da sakon jihar.
Daraktan Hukumar Sani Anas ne ya bayyana haka bayan kammala kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin majalisar dokokin Kano.
Sani Anas yace akwai kayayyakin aikin kashe gobara da dama da suka lalace a hukumar wanda duka za’a canza su da zarar an amince da kasafin da suka yiwa hukumar shekarar mai kamawa.
Shima Shugaban hukumar KAROTA Faisal Mahmud Kabir bayan kare kasafin kudin hukumar na shekara mai zuwa, ya ce al’ummar Kano zasu ga sauyi a yanayin yadda jami’an hukumar suke gudanar da ayyukan su a tituna la’akari da matakan da shugabancin hukumar yake dauka musamman a bangaren kwarewar aiki.
Suma Shugabannin gidajen rediyo na Kano da gidan talabijin na Abubakar Rimi Hajiya Hauwa Ibrahim da Abubkar Adamu Rano dukkanin su sun kare kasafin kudin ma’aikatun nasu a gaban kwamitin zauren majalisar dokokin ta Kano.
