
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu matasa maza da mata biyar bisa zargin gudanar da bikin aure ba tare da amincewar iyaye ko bin ka’idojin aure na Musulunci ba.
Rahotanni sun ce, Aminu mai shekara 23, saurayin da ake zargi, ya auri budurwarsa Sadiya mai shekara 22, inda aka gudanar da auren akan sadaki na Naira 10,000 ba tare da izinin iyayensu ba.
Sauran matasan da suka shiga cikin lamarin sun hada da Umar mai shekara 24 wanda ya wakilci ango, da kuma Abubakar mai shekara 23 wanda ya wakilci waliyyin amarya, da kuma Usaina mai shekara 21 da Karin wasu mata da suka shaida daurin auren.
Mataimakin kwamandan Hisbah, Dakta Mujaheedden Aminuddeen Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce, “sun dauki mataki ne bayan rahotannin da mazauna yankin suka bayar.
It is further emphasized that this action contravenes both Islamic teachings and the laws of the Kano State regarding marriage. The Hisbah board will persist in taking appropriate measures against anyone who engages in unlawful marriage practices. Currently, those accused are being held at the Hisbah office to facilitate ongoing investigations. The commitment to uphold legal and moral standards remains paramount in ensuring compliance within the community. Ya kuma bayyana cewa wannan aiki ya sabawa koyarwar Musulunci da dokokin jihar Kano kan aure, kuma hukumar za ta ci gaba da daukar mataki kan duk wanda ya yi aure ba bisa doka ba. Yanzu haka ana tsare da wadanda ake zargin a ofishin Hisbah don ci gaba da bincike”.
A ‘yan watanin baa, hukumar ta kama wasu matasa da irin wannan laifin.