
Shugabannin ƙasashen Birtaniya, Faransa, da Canada sun fitar da sanarwa ta haɗin gwiwa, inda suka yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta ɗauka na faɗaɗa ayyukan soji a zirin Gaza, suna mai cewa wannan lamari bai dace ba.
A cikin sanarwar, ƙasashen sun jaddada cewa idan har ba a dakatar da hare-haren ba tare da ɗage haramcin shigar da kayayyakin agaji cikin yankin ba, za su fara nazarin matakan da za su ɗauka kan Isra’ila.
Haka kuma, shugabannin sun nuna goyon bayansu ga yunƙurin tsagaita wuta da Amurka ke jagoranta, tare da yin kira ga ƙungiyar Hamas da ta gaggauta sakin duk mutanen da ta yi garkuwa da su.
Sanarwar ta nuna damuwar ƙasashen kan ci gaban rikicin da ke ƙara jefa yankin cikin yanayi mai tsanani, tare da kira ga sasantawa da zaman lafiya.