Wasu yara a jihar Borno sun nannado harsasan harbo jirgin sama a ragar kama kifi a yankin Bulunkutu na Maiduguri.
Majiyoyi a yankin sun yi zargin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka jefar da harsasan, inda mazauna suka sanar da hukumomin tsaro, wanda ya sa sojoji suka killace wurin.
Wani mazaunin garin, Malam Bashir, ya ce: “Abin da ya firgita yawancin mazauna shi ne cewa ‘yan Boko Haram sun taɓa zama a wurin kafin rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta kore su.”
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake fargabar tsaro a Borno da jihohin Yobe da Adamawa, inda aka samu munanan hare-haren bama-bamai da kuma dakile hare-haren ƙunar baƙin wake a ‘yan makonnin baya-bayan nan.
Sai dai rundunar sojojin Operation HADIN KAI ta tabbatar da cewa an kama wanda ake zargi da jagorantar kai hare-haren bama-bamai, wanda ya kashe mutane biyar tare da raunata wasu 34 a lokacin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a wani masallaci a Maiduguri.
