Wasu ‘yanbindiga sun shiga wasu kauyukan Biresawa da Sundu a Karamar Hukumar Tsanyawa , sun kuma yi awon gaba da wasu mata da yara guda 10.
Lamarin ya faru ne a daren Litinin da misalin karfe 10, a cewar wani mazauni garin, a hirarsu da wakilinmu.
“Muna zaune a waje ne muna hira sai suka shigo garin, da ganinsu sai duk muka gudu. Mata na cikin gida su basu san abin da ke faruwa ba. Sai suka shige gidajen suka kwashe matan suka yi gaba da su”. In ji shi
Magidancin ya kuma ce a gidansu kadai ‘yan bindigar sun dauke matarsa da kuma ‘yarsa da matar yayansa da matan ‘yan uwansa biyu.
Suka kuma kara da wasu kauyen kusa da su.
Dangane da yadda ‘yanbindigan suka zo musu, ya ce da mashin suka suka zo, amma a kafa suka shigo garin na su kasancewar sun bar mashina na su a wani kauyen kusa da su da ke yankin jihar Katsina.
Ya kara da cewa jami’an tsaro zo bayan ‘yanbindigan sun tafi, sun kuma basu bayanan duk abin da ya faru.
Har kawo yanzu haka dai babu wata sanarwa daga rundunar yansandan Kano kan faruwar lamarin.
