Hukumomin tsaro a jihar Kano, sun gargadi mutane da su kaucewa shiga cunkoson jama’a sakamakon samun bayanan sirri kan yunkurin kawo hare-hare jihar da wasu yan ta’adda ke shirya wa.
Kakakin rundunar yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana a wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a ranar Juma’a.
Sanarwar ta yi kira da a kauracewa dukkan wuraren taruwar jama’a zuwa wni lokaci, don dakile wa da kuma bankado masu yunkurin kawo hare-haren.
SP Abdullahi Haruna, ya kara da cewa domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano, an dauki duk shirin da ya kamata na tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Haka zalika an baza jami’an tsaro na musamman wadanda suka kware wajen ganowa da kuma dakile ayyukan yan ta’adda.