
Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi tare da kwato kudin fansansa Naira miliyan 4, da dubu dari 8 da dubu 50 daga hannun masu garkuwa da mutane.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Ibrahim Adamu Bakori, ne ya jagoranci aikin ceto wanda aka sace a garin Zakirai da ke Karamar Hukumar Gabasawa.
A cewar kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, masu garkuwar sun fara bukatar kudin fansa na Naira miliyan 15 kafin jami’an tsaro su kai samame, su kama mutane biyar da ake zargi, tare da kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.
An ceto mutumin ne a ranar 17 ga watan Maris, sannan aka mayar da kudin da aka kwato ta hannun shugaban karamar hukumar Gabasawa, Sagir Usman Abubakar, wanda ya gode wa rundunar a madadin mutumin da al’ummar yankin.
Kwamishinan ’yan sandan ya bukaci jama’a da su kasance masu sa ido tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi domin hana aikata laifuka a jihar.