Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta jaddada cewa ba za ta sassauta wa duk wanda aka samu da hannu a laifukan ta’addanci a sassan jihar ba.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin wani biki na ƙarin girma ga jami’an ’yan sanda 13.
Jami’an da suka samu ƙarin girman sun haɗa da mukaddashin Kwamishinan ’Yan Sanda, Mataimakan Kwamishinan ’Yan Sanda, da kuma Sufuritanda.
A jawabinsa, CP Bakori ya taya jami’an da suka samu ƙarin girman murna, tare da jan hankalinsu kan ƙara zage damtse wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce rundunar ’yan sanda ta ƙara ɗaukar tsauraran matakai domin dakile ayyukan miyagu da kuma hana duk wani yunƙurin ta’addanci a fadin jihar.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da bayanan sirri, domin magance matsalolin tsaro, musamman barazanar shigowar ’yan bindiga daga Jihar Katsina.
CP Bakori ya bayyana cewa rundunar ta kai samame zuwa dazukan da ake zargin ’yan ta’adda na amfani da su wajen shigowa jihar Kano ta kananan hukumomin Shanono, Bagwai da Tsanyawa, domin dakile duk wani yunƙuri na shiga jihar.
