Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta kama wani mutum mai suna Ahmed Abubakar mai shekara 32 bisa zargin ƙoƙarin kai harsasai guda 1,000 ga ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.
Kwamishinan ‘yan sanda na Abuja, Miller Dantawaye, ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma, a Unguwar Dodo, Karamar Hukumar Gwagwalada, bayan samun sahihin bayanan sirri.
Binciken farko ya nuna cewa Ahmed Abubakar yana mu’amala da wani abokinsa Yusuf Mohammed, inda aka gano cewa suna shirin sayo harsasai domin kai wa ‘yan bindigar a Zamfara.
Kwamishinan ya jaddada kudirin rundunar na dakile masu aikata laifuka a Abuja da kewaye, tare da tabbatar da tsaron mazauna yankin.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abin da ake zargin laifi ta layukan gaggawa na rundunar.
