Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta karyata shigar ‘yan bindiga Dutse, babban birnin jihar.
Mai Magana Da yawun Rundunar, SP Shi’isu Lawan Adam ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta bayyana rahoton a matsayin na bogi, mai ruɗarwa, kuma an ƙirƙire shi ne don tayar da hankalin jama’a.
Domin wadanda aka gani mafarauta ne daga jihar Bauchi.
“Bincike ya gano cewa, mutanen da ke cikin bidiyon ‘yan Kungiyar Tsaro ta Farauta ne (Peace and Security Service Organisation) daga Jihar Bauchi, waɗanda ke komawa daga wani taro da aka gudanar a Chai-Chai Sabuwa, a Karamar Hukumar Ringim.
“An gan su ne da kayan aikinsu na gargajiya irin su bindigogin farauta (Dane guns), baka, da kibau.” In ji shi.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ba da kariya ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yi kira ga mutane da su zauna lafiya, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Su kuma ci gaba da ba da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar isar da bayanai masu inganci da lokaci.
