Aminu Abdullahi Ibrahim
‘Yan kasuwar Rano a Jihar Kano sun yi kira ga majalisar dokokin jihar Kano da ta ci gaba da bincike kan shugaban karamar hukumar Rano, Alhaji Muhammad Nazir Ya’u, bisa zargin rushe musu shaguna da aka yi a kasuwar.
Shugaban tsohuwar kasuwar Rano Alkasim Hamza Madaci, ne bayyana hakan a yayin zantawarsa da Premier Radio.
Ya ce sakamakon rushe shagunan ‘yan Kasuwar ya jefa da dama cikin matsananciyar damuwa, sakamakon asarar jari da suka yi, wanda hakan ya shafi harkokin kasuwancinsu da rayuwarsu gaba ɗaya.
Idan za a iya tunawa a shekarar da ta gabata ne, majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar sakamakon korafe-korafe da aka gabatar mata, ciki har da na ‘Yan kasuwar da suka koka kan wasu zarge-zarge da suka shafi gudanar da mulki.
