
Wasu ‘yan bindiga sun hallaka Hakimin Garin Dogon Daji, wani kauye a yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
A wani mummunan hari da suka kai da yammacin jiya, Litinin.
Rahotanni daga yankin sun tabbatar da cewa maharan sun afka garin ne inda suka kashe hakimin ta hanyar yanka shi a bainar jama’a, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici da fargaba.
Shugaban karamar hukumar Tsafe, Alhaji Garba Shehu Tsafe, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai.
Ya Kuma ce wannan ba shi ne hari na farko da ake kaiwa yankin ba, inda ya ce ‘yan bindigar sun kuma tare wasu manyan hanyoyi da ke kaiwa zuwa birnin Gusau.
Ya alakanta karuwar hare-haren yankin da sulhun da ake yi a jihar Katsina mai makwabtaka da Zamfara.