
Wasu ’yan bindiga sun sake kai hari a garin Faruruwa, dake yankin ƙaramar hukumar Shanono.
Maharan sun kai harin ne a ranar Talata da Magariba Sun kuma suka kashe mutum ɗaya tare da awon gaba da dabbobin al’umma masu yawa.
A cewar wata majiya a hirarsu da wakilinmu, ‘yan bindigan sun shigo garin ne kan babura sama da guda 25, kowannensu ɗauke da mutum uku, kuma dauke da bindigogi.
“Sun shigo ne ta santar (wata unguwa da ake kira) Abuja sai suka biyo wata unguwa ta Fulani da ake ce mata Bilbe, daga nan suka kwashe shanun mutane da yawa…
“Shi wannan da aka harbe a nan ‘Yan lamba din, ya zo zai wucewa ne a mashin suka harbe shi.” In ji wani mazaunin garin a hirarsa da wakilinmu.
Majiyar ya ce suna zargin ‘yan bindigar sun shigo ne daga jihar Katsina.
Babu rahoton ‘yan bindigan sun sace wani mutum don neman kudin fansa, sai dai shigowar ta su ya bar mazauna garin cikin firgice da tashin hankali a cewar majiyarmu.
Jami’an tsaro sun isa garin bayan da ‘yan bindigar sun tafi.
“Kuma jami’an tsoron ko da sun zo babu abin da za su iya yi musu saboda ‘yan bindigar sun fi karfin su saboda irin muggan makaman da suke dauke da shi jami’an tsaron ba su da shi”. In ji majiyar
Ya kuma ce, jami’an tsaron da suke da su a garin ba su da yawan da zu tunkari ‘yan bindigan.
Kawo yanzu babu wani Karin bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar Kano kan faruwar lamarin.