La’akar da cewa farashin na suka daga manyan kamfanoni da kuma amafanin gone da aka samu
Ministan Noma na Tarayya Abubakar Kyari ne ya yi wannan kiran a jiya Talata a wurin bikin ranar kaddamar da noman Alkama na shekarar 2025, wanda gwamnatin jihar Jigawa ta shirya a Karamar Hukumar Ringim.
“Gwamnatin tarayya na sane da faɗuwar farashin kayan abinci a faɗin manyan kasuwanni, musamman na kayan masarufi kamar su shinkafa da taliya.
“Don haka yakamata masu shaguna a unguwanni da masu burodi su saukaka wa ‘yan kasa tun da suma sun samu saukin a maimakon ci gaba da tafiya jiya I yau a batun farashi”. In ji shi.
A farkon makon nan kungiyar ‘yan kasuwar Singa da ake sayar da kayan masarufi suka nesanta kansu da tsadar kayayyaki a kasuwanni.
Sun dora laifin akan masu sayar da kayayyakin a unguwanni da kanana shaguna.
