
Ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Kasa, PENGASSAN ta amince da jingine yajin aikin da ta shiga bayan samun saɓani da matatar mai ta Dangote
Yajin aikin ne zuwa ne bayan PENGASSAN ta zargi mattaar da korar fiye da ma’aikata 800 saboda sun nuna sha’awar shiga ƙungiyar.
Gwamnatin tarayya ce ta shiga tsakani a sasancin ɓangarorin biyu da ake yi tun ranar Litinin, to amma sai a yau Laraba ne aka cimma matsaya.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar kwadagon ƙasar ta fitar ta ce matatar ta amince da mayar da ma’aikatan da ta kora domin su ci gaba da aiki da ita.
A nata ɓangare, ƙungiyar ta PENGASSAN ta ‘amince ta fara shirye-shiryen janye yajin aikin”.
Tun bayan fara aikin matatar Dangote a 2024 ta riƙa cin karo da rassan ƙungiyoyin ƙwadago a fannin man fetur na ƙasar, wadanda ke zarginta da ƙoƙarin mamaye harkokin kasuwancin man fetur a ƙasar.