Rundunar ’yan sanda ta ƙara tsaurara matakan tsaro a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, gabanin ziyarar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
Rahotanni sun ce rundunar ta tura jami’an tsaro ɗauke da manyan makamai, tare da motocin yaƙi masu sulke zuwa wasu muhimman wurare a cikin birnin, domin tabbatar da tsaron Mataimakin Shugaban Ƙasar da sauran jami’an da za su halarci jihar.
Haka kuma, an ƙara yawan jami’an tsaro a kan hanyoyin da ake sa ran tawagar Mataimakin Shugaban Ƙasar za ta bi, yayin da jami’an ke sa ido kan zirga-zirgar ababen hawa da ayyukan jama’a a yankunan da abin ya shafa.
Ana sa ran ziyarar Shettima za ta kasance domin jajantawa iyalan mamatan da sauran al’ummar jihar, yayin da jami’an tsaro suka ce matakan da aka ɗauka na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin ziyarar.
Hukumomin tsaro sun kuma shawarci mazauna Yola da su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai tare da bin umarninsu, domin tabbatar da gudanar da ziyarar cikin kwanciyar hankali.
