
Mako guda bayan komawarsa ofis daga dakatarwar da shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi masa gwamnan Rivers, Similayi Fubara, ya sauke shugabanni da mambobin hukumar fansho na jihar.
Gwamnan ya sanar da rushe shugabancin hukumar a wata sanarwa da shugabar ma’aikatan jihar Mrs Inyingi S.I Brown ta fitar a yammacin ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce an baiwa Babban akanta janar na Rivers ikon cigaba da kula da aiyukan hukumar.
Ta kuma umarci wadanda aka sauke su mika ragamar aiki ga daraktan mulki na hukumar ta Fansho.