
Shugaba Tinubu ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara, a wani zama na sirri da suka yi a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.
Tinubu ya gana da gwamnan ne a yammacin Litinin bayan mayar da shi kan mulki.
Gwamna Fubara dan jam’iyyar adawa ta PDP, ya isa fadar shugaban ƙasa ne da misalin karfe 6:20 na yamma.
Wannan shi ne zaman ganawarsu na farko da Shugaba Tinubu bayan wata takaddama ta siyasa da ta dabaibaye jihar wadda ta sa aka nada Kantoma don gudanar mulkin jihar na tsawon watanni watanni shida.
Babu wani bayani kan ganawar ta su, sai dai ana ganin ba za ta rasa nasaba da siyasar jihar ta Rivers ba.
Zaman nasu na zuwa ne bayan wasu muhimman ganawa da Shugaba Tinubu ya yi da AbdulRahman AbdulRazaq Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara da Gwamnan Imo Hope Uzodimma da kuma Tajudeen Abbas, Shugaban Majalisar Wakilai, tare da wasu fitattun jami’an gwamnati a Abuja.