Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen mutane biyu zuwa majalisar dokokI domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar yau Lahadi a nan Kano.
Wadanda aka mika sunayensu sun hada da Barista Abdulkarim Kabir Maude daga karamar hukumar Minjibir, mai shekara 40.
Sai kuma Dr. Aliyu Isa Aliyu – Mai Shirin zama Farfesa a fannin lissafi, mai shekara 41.
Dr Aliyu na ɗaya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin karatun waje na Kwankwasiyya, kuma ya taba rike mukamin sakataren kudi na jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano.