Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun daƙile harin da ’yan ta’addan ISWAP suka kai a garin Gamborun Ngala da ke kan iyakar Najeriya da ƙasar Kamaru.
Rahotanni daga rundunar sun nuna cewa an kai harin ne da misalin ƙarfe 6:15 na yammacin jiya Asabar, inda aka ji ƙarar harbe-harbe masu ƙarfi a sassa daban-daban na garin.
Sai dai a cewar majiyoyi, sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka shiga fafatawa da ’yan ta’addan, kuma suka fatattake su ba tare da wata asara a ɓangaren dakarun ba.
Rahotanni sun ce babu wani soja ko farar hula da ya rasa ransa ko ya jikkata, yayin da aka samu cikakken kwanciyar hankali a garin bayan da aka daƙile harin.
A yanzu dai, harkokin yau da kullum sun kankama a Gamborun Ngala, inda mazauna garin ke jinjina wa sojojin bisa jajircewarsu da nasarar da suka samu wajen kare al’umma daga wannan mummunan hari.
