
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Ta Kasa (SSANU) da kuma Kungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU) za su gudanar da zanga-zangar kwana daya a fadin kasar a gobe Alhamis, 9 ga watan Oktoba.
Kungiyoyin za su gudanar da zanga zangar ne kan gazawar gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin da suka dade suna bukatar gwamnatin ta warware.
Shugaban SSANU na Jami’ar North West kwamared Muhammad Jaji ne ya sanarwar da hakan, ya kuma ce daukar wannan matakin biyo bayan wani cikakken nazari da kwamitin hadin gwiwa na kungiyar ya yi ne a ranar 6 ga watan Oktoba, bayan karewar wa’adin da aka bai wa gwamnati.
“A nan jihar Kano gwamnati na kokari kan ma’aikata amma ya zama dole su yi biyayya ga uwar kungiyar su na shiga zanga-zangar ta gama gari”. In ji shi.
A wata takardar da aka mika wa daukacin shugabannin NASU da SSANU kwamitin hadin gwiwar kungiyar ya umurci dukkanin rassa da su gudanar da taron gaggawa a yau Laraba domin zaburar da ‘ya’yan kungiyar don gudanar da zanga-zanga a harabar jami’o’in jihar nan.