Sufeto Janar na ‘ƴan sanda Kayode Egbetokun, ya tabbatar da cewa an kama mutum 26 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi a al’ummar Yelwata da ke ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benue, ranar 13 ga Yuni, 2025.
Shuguban ‘yansanda ya ce, an tabbatar da mutuwar mutum 47 a cikin harin, yayin da wasu 27 kuma suka jikkata kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Rundunar ‘yan sanda ta ce, an kuma kashe wasu biyu daga cikin ‘yan harin a ranar da lamarin ya faru.
Egbetokun ya ce, an tura jami’an tsaro domin bin diddigin lamarin, kuma daga baya an kama wasu manyan masu hannu biyu-biyu a kisan wanda hakan ya kai ga kama karin mutum bakwai.
