
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa har yanzu babu wata motarta da aka bari ta shiga Gaza, duk da cewa Isra’ila ta sanar da karshen killace yankin sama da watanni biyu.
A yayin wani taron manema labarai a Geneva, Daraktar WHO na Gabashin Mediterrenean, Hanan Balkhy ta ce, fiye da makwanni 11 kenan ba a bar motocin WHO su shiga Gaza don tallafin kiwon lafiya, sai dai an bar daidaikun motocin agaji su shiga cikin ‘yan kwanakin nan.
Shugabar ta kuma ce, WHO na cikin damuwa kan yadda mutanen yankin ke cikin halin tagayyara da bukatun jinya, amma babu abin da za su iya yi, duk da cewa akwai manyan motoci 51 dauke da kayan jinya da ke kan iyaka.
Rahotanni sun bayyana cewa an amince da shigar motocin dakon kaya 400 zuwa Gaza, amma kawo yanzu 115 kacal suka samu damar isar da kaya, kuma babu motocin da aka bari su isa arewacin yankin, inda dakarun Isra’ila suka mamaye.
Lamarin na ci gaba da haifar da tsattsauran damuwa kan yanayin kiwon lafiya da jin dadin al’ummar Gaza, yayin da hukumomi ke kokarin hanyar warware matsalar.