
Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya sanar da cewa daga ƙarshen watan Yuli 2025, zai dakatar da tallafin gaggawa na abinci da kiwon lafiya ga fiye da mutum miliyan ɗaya a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya, sakamakon ƙarancin kuɗi.
Darektan shirin a Najeriya David Stevenson ne ya bayyana cewa, kayan abinci da na kiwon lafiya da ake rabawa sun ƙare gaba ɗaya, kuma rabon da ake ci gaba da bayarwa yanzu shi ne na ƙarshe da ke hannunsu.
“Tallafin zai tsaya daga ƙarshen Yuli, lokacin da ake tsammanin kayan abinci da na lafiya za su ƙare baki ɗaya,” in ji Stevenson.
Shugaban ya kuma ce, idan ba a samu gudunmawar kuɗi cikin gaggawa ba, akwai yiwuwar dubban mutane su fuskanci matsananciyar yunwa, su tsere daga gidajensu ko kuma su fada hannun kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Rahoton ya nuna cewa kusan mutum miliyan 31 ke fama da matsananciyar yunwa a Najeriya, adadi mafi muni da ƙasar ta taɓa fuskanta a tarihi.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da tashen hankali da rashin tsaro ke ƙaruwa a sassan Arewa maso Gabas, inda hare-hare daga ‘yan ta’adda ke cigaba da barazana ga rayuka da dukiyoyi.