Wani tsagi na darikar kadiriya a nan jihar Kano ya gurfanar da Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya bisa zargin bata musu suna.
Shugaban wani tsagi na Rabida Muhammadiyya kuma Shugaban majalisar koli na darikar kadiriya ta afrika Ibrahim Isa Abdullahi Makwarari ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Litinin din nan.
Ya ce malamin ya shiga kafafen yada labarai da na sada zumunta in da ya kalubalamci bikin takutaha da na maulidi da suke gudanarwa.
Lauyan masu kara Shehu Ahmad Tijjani ya ce tuni suka gurfanar da malamin kan zargin.
To sai dai ana sa banagaren lauyan wanda ake kara BL Kankarofi yace ba zai yi Magana ba tun da batun na gaban kotu.