
Malaman addinin Musulunci daga faɗin Arewacin Najeriya sun kammala wani taro na rana guda a Kaduna, wanda suka kira mai muhimmanci a halin da yankin ke ciki a kasarnan.
Malamai daga ƙungiyoyin Musulunci daban-daban da sarakuna da ‘yan siyasa da kuma sauran masu ruwa da tsaki ne suka halarci taron a Kaduna a ranar Laraba.
Maƙasudinsa babban taron shi ne haɗa kai don ɗaukar matakan da suka dace don magance matsalar tsaro da kuma na tattalin arziki da ke ta’zzara a yankin.
Matsalar tsaro
Mahalarta taron sun yi musayar ra’ayoyi kan musabbabin matsalar tsaro da lalubo hanyoyin maganceta da kuma irin rawar da shugabannin addini ya kamata su taka don gano mafita mai ɗorewa.
Dakta Bashir Aliyu Umar, Limamin masallacin Alfruqan na Kano kuma shugaban Kwamitin Ƙoli na addinin Musulunci a Najeriya, a jawabinsa a taron, ta’aliƙi yayi kan ƙaruwar satar mutane da ‘yan fashin daji da kuma matsin tattalin arziki a faɗin yankin.
Malamin ya jaddada buƙatar malaman addini da shugabannin siyasa da kuma sarakuna su haɗa-kai don ceto rayuka da dawo da zaman lafiya a yankin.
“Dole mu ajiye bambance-bambancenmu. Dukkanmu Allah na Ya yi mu. Wannan taron maƙasudinsa shi ne haɗin-kai ba rashinsa ba”. In ji shi
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdullaziz Yari ya yabi taron da cewa an yi shi a kan gaɓa, kasancewar rashin tsaro ya ƙi ci, ya kuma ƙi cinyewa a arewa saboda rashin tsari da rashin damarmakin tattalin arziki da Kuma labaran ƙarya.
“Ba zai yiwu mu yi ta zargin gwamnati ba. Miyagun dake assasa komai suna cikinmu.
“Dole ne mu yi aiki tare daga kan malamai har zuwa ‘yan sauran ƙasa domin kawo ƙarshen wannan bala’i,” in ji Yari.
Tsohon gwamnan ya kuma yi kira kan a sauya ɗabi’u na tsarin tattalin arziki, yana mai cewa halayyar nan ta neman son yin kuɗi cikin gaggawa na taimakawa wajen ƙaruwar miyagun laifuka da rashin zaman lafiya.

Haɗin kan Musulmai
Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na III, ya buƙaci malaman addini su dage wajen cigaba da yaɗa saƙonnin zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmai a fadin ƙasar, bisa ga koyarwar Musulunci.
Sheikh Gumi kuwa, jaddada muhimmancin samun tattaunawa a tsakanin bangarorin Musulmi ya yi.
“Wannan taron ba ya adawa da kowa, sai don ci gaban ƙasa. Tattaunawa na da muhimmanci.
“Idan arewacin Najeriya ya zauna lafiya, to ƙasar gaba daya za ta amfana,” in ji shi.
‘Yan majalisar wakilai da na dokoki da suka samu halartar taron sun sha alwashin ba da hadin kai don cim ma muradun taron sosai.