Wasu daga cikin ’yan Majalisar Tarayya sun nuna damuwa cewa sabbin dokokin haraji ba su yi daidai da waɗanda Majalisar Ƙasa ta amince da su ba.
Batun ya fara ne bayan wani ɗan majalisa, Abdulsammad Dasuki, ya zargi cewa dokokin harajin da aka fitar sun ƙunshi sauye-sauyen da ba a tattauna ko amince da su a majalisa ba.
Ya ce hakan ya saɓa wa tsarin dokoki tare da haifar da damuwa game da kundin tsarin mulki.
Wasu ’yan majalisa biyu, Muhammad Bello Fagge da Yusuf Shitu Galambi, sun goyi bayan wannan zargi, inda suka yi gargaɗin cewa irin waɗannan sauye-sauyen na iya raunana dimokiraɗiyya da rage amincewar jama’a ga gwamnati.
Sun ce wasu sassa na dokokin na nuna an bai wa ɓangaren zartarwa, musamman Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa, fifiko fiye da ƙima ba tare da isasshen sanya ido daga majalisa ko kotuna ba.
Galambi, ya yi kira da a dakatar da aiwatar da dokokin harajin, waɗanda aka shirya fara amfani da su a watan Janairun 2026, har sai kwamitin Majalisar Wakilai ya kammala bincikensa
