Kungiyar ECOWAS ta dakatar da ma’aikatanta daga kasashen Sahel—Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.
Hakan ya biyo bayan ficewar kasashen daga kungiyar da wa’adin ya cika.
A wata sanarwa da Kungiyar ta bayar, ta tabbatar da cewa an mikawa ma’aikatan takardun sallama a hukumance, wanda hakan ke nuna cewa sun daina aiki da kungiyar.
Kasashen uku sun fice daga ECOWAS ne a Janairu shekarar 2024.
Duk da haka, sun bayyana cewa a shirye suke da su tattauna da ECOWAS tare da ba ta fifiko ga muradun al’ummarsu.
