Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyya ga fitaccen ɗan damben duniya, Anthony Joshua, bayan wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi, inda mutane biyu daga cikin abokan rakiyarsa suka rasa rayukansu.
A wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.
Haka kuma, ya yi wa Anthony Joshua fatan samun sauƙi cikin gaggawa, bayan da ya tsallake hatsarin da ƙananan raunuka.
Shugaban ya bayyana hatsarin a matsayin babban iftila’i da ya ɗaga hankalin jama’a, yana mai jaddada cewa Anthony Joshua abin alfahari ne ga Najeriya.
Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya ta tabbatar da cewa fitaccen ɗan damben ɗan Birtaniya dan asalin Najeriya ya yi hatsarin mota ne a kan titin Legas zuwa Ibadan, inda mutane biyu suka mutu a wurin.
Rahoton ya ce Joshua ya tsira da ƙananan raunuka.
