Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa shi ne ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya sauya masa wurin aiki daga Jamus zuwa Afirka ta Kudu.
Fani-Kayode ya bayyana hakan ne yayin wata liyafa da ofishin jakadancin Najeriya a Pretoria ya shirya, bayan miƙa takardun fara aikinsa ga Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, a ranar 13 ga Nuwamban 2026.
Ya ce ya zaɓi Afirka ta Kudu ne saboda muhimmancin da ƙasar da Najeriya ke da shi wajen bunƙasa tattalin arziki da ci gaban yankin Afirka.
A cewarsa, ya nemi Shugaba Tinubu ya sauya masa wurin aikin, kuma shugaban ya amince da buƙatarsa.
Fani-Kayode ya ce Najeriya da Afirka ta Kudu ƙasashe ne masu tarihi da al’adu masu ƙarfi, don haka ya kamata su ƙarfafa alaƙarsu tare da guje wa duk wani abu da zai haddasa rashin fahimta ko rarrabuwar kai.
Tun da farko, an naɗa tsohon ministan a matsayin jakadan Najeriya a Jamus, kafin daga bisani a sauya masa wurin aiki zuwa Afirka ta Kudu a watan Mayun 2026.
A wancan lokacin, tsohon ministan ya bayyana cewa ya gabatar da buƙata a hukumance ga tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa da tura shi Jamus saboda wasu dalilai na kansa da kuma kasancewar ya shafe mafi yawan rayuwarsa a Turai.
Ya ce ya fi son zuwa Afirka ta Kudu, ƙasar da bai taɓa ziyarta ba, amma yake da matuƙar sha’awar saninta.
