
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya bayyana cewa ya haƙo rijiyoyin man fetur guda huɗu a yankin Kolmani da ke Jihar Bauchi, a wani mataki na ci gaba da ƙoƙarinsa na bunkasa albarkatun mai da iskar gas a Najeriya.
Shugaban Sashin Haɓaka Albarkatun Mai da Gas na kamfanin, Injiniya Yusuf Usman, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da aka gudanar a Kaduna.
Taron dai na tattaunawa kan hulɗar gwamnati da al’umma, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya.
Usman ya ce NNPCL na ɗaukar matakai masu muhimmanci wajen ganin an samu nasarar hako albarkatun ƙasa, musamman a yankin Arewa, tare da tabbatar da cewa kamfanin na jajircewa wajen aiwatar da shirye-shiryensa a fadin ƙasar.
A cewarsa, domin goyon bayan shirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da iskar gas a matsayin madadin mai (CNG), ana gina matatun sarrafa iskar CNG da kuma iskar gas zuwa LNG guda biyar a Jihar Kogi.
“Wannan na daga cikin matakan da za su taimaka wajen samar da iskar gas da kuma sauƙaƙa samun ta a fadin yankin Arewa,” in ji shi.