Burtaniya da Afrika ta Kudu sun mayar da wasu kayayyakin tarihi 130 na zinare da tagulla da aka sace su a lokacin mulkin mallaka.
Kayan da aka dawo da su sun haɗa da kayan sarauta da ganguna da kayyakin zinare na al’ada, waɗanda aka yi su tun a shekarun 1870, suna kuma nuna muhimmancin zinariya a al’adar Asante.
Sarkin Asante na Ghana, Otumfuo Osei Tutu II, ya bayyana farin cikinsa dangane da wannan muhimmain mataki na dawo da kayayyakin.
A jawabin Sarkin, ya gode wa AngloGold Ashanti bisa mayar da kayayyakin da aka saya bisa doka, yana mai cewa hakan alama ce ta “girmamawa da ɗorewar al’adun masarautar Asante.
“Babu shakka wannan ya nuna irin arzikin da Ghana ke da shi tun tale-tale, kuma waɗannan kaya za su ƙara mata ƙaimi wajen alkinta kayanta na tarihi”. In ji shi.
Wannan dai ba shine karon farko da Burtaniya ke mayar da kayan tarihi zuwa wasu ƙasashe musamman na yammacin Afrika ba.
An mika kayayyakin ne a fadar Manhyia da ke birnin Kumasi, inda kamfanin hakar ma’adinai na Afirka ta Kudu, AngloGold Ashanti, ya bayyana cewa wannan mataki na a matsayin nuna girmamawa da neman sulhu da al’ummar Asante.
Bayanai sun ce cikin wannan adadi Burtaniya ta maido da guda 25, yayind Afrika ta Kudu ta mayar da sama da 100.
