Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL, Mele Kyari, ya bayyana matakin da kwamitin majalisar dattawa kan asusun jama’a ya ɗauka na fitar da sammacin kama kamashi a matsayin abin mamaki dangane da binciken da ake yi kan bacewar wasu kuɗaɗen kamfanin.
A wata wasiƙa da ya aikewa shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a, Kyari ya bayyana cewa tun da farko ya sanar da kwamitin cewa ba zai iya halartar zaman majalisar ba sakamako karɓar magani a ketare.
“Na samu labarin sammacin kama ni da aka fitar a kaina yayin zaman kwamitinku a yau, 10 ga Yuni, 2026. Wannan lamari ya ba ni mamaki matuƙa,” in ji shi.
Kyari ya ce ya sanar da kwamitin a hukumance ta wata wasiƙa mai kwanan wata 11 ga Mayu, 2026 cewa yana karɓar magani a wajen Najeriya.
Ya ƙara da cewa ya bayyana aniyarsa ta halartar gayyatar kwamitin da zarar ya dawo ƙasar, tare da bayar da damar amsa tambayoyi cikin gaggawa ta hannun lauyoyinsa.
Kwamitin majalisar dattawa kan asusun jama’a ya fitar da sammacin kama Kyari bayan bai halarci zaman da aka shirya ba kan binciken bayanan kuɗin NNPCL, ciki har da batun sama da Naira tiriliyan 210.
An gabatar da kudurin fitar da sammacin ne daga Victor Umeh tare da goyon bayan Adams Oshiomhole.
Sai dai Kyari ya jaddada cewa ba shi da abin ɓoyewa kuma ya taimaka wa Majalisar Dattawa kan binciken.
