
Gwamnatin jihar Kano ta ce, tuni ta shirya domin fara tattara alkaluman wadanda suka mutu da kuma karuwar Al’umma da ake samu a jihar nan.
Gwamnatin jihar Kano ta ce, tuni shirye-shirye suka yi nisa domin fara tattara alkaluman wadanda suka mutu du kuma karuwar Al’umma da ake samu a jihar nan.
Shugaban hukumar kididdiga na jihar Kano Dakta Surajo Suleman ne ya bayyana hakan a hirarsa da Premier radio.
Dakta Surajo Suleman ya kara da cewa, aikin tattara alkaluman zai ba wa gwamnati damar kai wa al’umma daukin gaggawa akan abin da suke da bukata.
“Akwai shirin da muke yi na fara gudunar da kidayar magidanta da kuma gidaje a fadin jihar Kano. In ji shi.
Dakta ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba wa gwamnati dukkanin hadin kan da ake da bukata domin ganin an cimma nasarorin da aka sanya a gaba.