Masar ta gargaɗi cewa goyon bayan da Isra’ila ke bai wa shirin shugaba Trump na kwashe Falasɗinawa daga Gaza na iya kawo cikas ga tattaunawar tsagaita wuta.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta ce, kalaman wasu jami’an gwamnatin Isra’ila na nuna yunkurin zai tunzura ɓangarorin biyu su komawa filin daga.
Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa ma ta nuna damuwa kan kudurin.
Kakakinta, Jamal Rushdie, ya ce Hamas da Falasɗinawa za su iya yin watsi da tattaunawar su sake koma fada da juna.
Tun farko, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya umurci sojojinsa da su fitar da tsari kan ƴan Gaza da suka fice daga yankin da kansu.
