
Hakan ya sa ta samu wakilcin shiyyar Arewa Maso Yamma a gasar kasa baki daya a Abuja.
‘Yan wasan kwallon kafa na ‘yan kasa da shekara 13 da suka wakilci jihar Kano sun lashe gasar kwallon kafa da Hukumar ilimin bai-daya ta kasa UBEC ta shirya .
‘Yan kwallon na Kano sun samu nasarar lallasa ‘yan wasan na Kaduna da ci daya mai ban haushi.
An kammala gasar wasannin ta kasa da hukumar ta shirya wa jihohin shiyyar Arewa maso yamma ne a Dutsen jihar Jigawa.
A wasan Kwallon Kwando na maza, daliban jihar Kano sun zo na biyu, bayan karawa da Jihar Sokoto.
A kuma Kwallon Hannu na maza da mata nan ma jihar Kano sun yi na biyu bayan sun kara da takwarorinsu na jihar Jigawa da kuma Katsina.
Sakamakon samun wannan nasara, daliban za su wakilci shiyyar Arewa maso yamma a makamanciyar gasar ta kasa wadda Hukumar ilimin bai daya ta kasa UBEC ta shi a Babban birnin tarayya Abuja.