Jami’an tsaron Turkiyya na ci gaba da aikin gano masu tsattsauran ra’ayin Islama da ake zargi da hannu a wani mummunan hari da aka kai wa sojoji a ranar Litinin, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji uku.
Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Ali Yerlikaya, ya sanar da cewa da safiyar ranar Laraba jami’an tsaro sun sake kama mutum 125 da ake zargin mambobin ƙungiyar IS ne.
Ya ce an kama mutanen ne a wani samame na haɗin gwiwa da hukumomin tsaro suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewarsa, adadin mutanen da aka kama ya haura 500 tun bayan da hukumomi suka sanar a makon da ya gabata cewa sun samu bayanan sirri kan yiwuwar kai hare-hare a lokacin bukukuwan Kirsimati da Sabuwar Shekara.
