
Jagoran ‘yan bindiga Bello Turji ya saki mutum sama da 100 da yake tsare da su a wani sabon yunkuri na samar da zaman lafiya da kawo karshen tashin hankali a Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa sakin mutanen ya biyo bayan dogon tsarin tattaunawa da amincewa da shirin sulhu da ake gudanarwa a yankin Arewa maso Yamma.
Zagazola Makama ne ya wallafa a shafinsa na X, a ranar Talata
“Wadanda aka sako sun hada da maza, mata da yara, kuma an mika su ga hukumomin yankin kafin kai su asibiti domin binciken lafiyar su.
“Majiyar tsaro ta shaida cewa wannan mataki na Bello Turji ya samo asali ne daga sakamakon tattaunawa mai zurfi tsakanin kungiyarsa da shugabannin al’umma da masu shiga tsakanin.
“Wata majiya da ta shiga cikin tattaunawar ta bayyana cewa an fara sakin mutane 36, sannan daga baya aka kara sakin wasu takwas, wanda ya kai jimillar 46 a matakin farko. Daga baya kuma aka ci gaba da sakin sauran, har adadin da aka sako ya kai sama da mutum 100 baki daya.” In ji shi.
Majiyar ta kara da cewa ana sa ran karin sakin mutane cikin kwanaki masu zuwa yayin da ake cigaba da tattaunawa.
Daya daga cikin masu sulhun ya ce wannan na iya zama babban mataki na farko wajen kawo karshen rikice-rikicen da suka dade suna hana al’umma zaman lafiya a Zamfara da kewaye