
Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa fitinannen ɗan ta’adda Bello Turji ya bukaci Naira miliyan 50 daga mazauna yankunan Zamfara da Neja kafin ya ba su damar fara noma a bana.
Wani rahoto daga shafin Bakatsine a X (Twitter) ya bayyana cewa Turji ya nemi wadannan makudan kuɗi ne a matsayin sharadi daga al’umma domin samun damar yin noma cikin kwanciyar hankali.
JKan haka, manoman yankin sun sake mika ƙokensu ga gwamnatin tarayya na neman dauki domin kawo ƙarshen wannan matsala.
Bello Turji na daga cikin fitattun ‘yan ta’adda dake addabar yankunan Zamfara da Sokoto da kuma Katsina, inda ya fi shahara wajen karɓar haraji daga manoma ko kuma hana su fita filayen noma idan ba su biya ba.
Al’ummomin karkara da dama a Arewacin Najeriya sun dade suna fama da irin wannan matsin lamba daga ‘yan bindiga, tare da neman daukin gaggawa daga gwamnati domin kawo ƙarshen wannan barazana ga rayuwarsu da tattalin arzikinsu.