
Tsohon Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa, zai ƙaddamar da sabuwar littafinsa mai suna The Shadow of Loot and Losses, wanda ke bayani kan badakalar aringizon kuɗi a tsarin tallafin man fetur a Najeriya.
“Littafin ya fallasa dabarun da aka yi amfani da su wajen wawure biliyoyin Naira da sunan shigo da Mai na bogi, maimaita karɓar kuɗi daga gwamnati, da kuma karkatar da mai zuwa ƙetare.
“Littafin ba kawai zai bayyana tarihin badakalar fetur ba, har ma zai zama kira zuwa gaskiya da ingantaccen tsarin tafiyar da kuɗin gwamnati”. In ji shi.
Bawa ya shugabanci EFCC daga 2021 zuwa 2023, inda ya jagoranci binciken badakalar tallafin mai na 2012, lamarin da ya janyo cece-kuce a fannin tattalin arzikin ƙasar.