Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki, tare da dimbin magoya bayansa.
Bafarawa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake jawabi a wani babban taro da aka gudanar a ɗakin taro na gidansa da ke Jihar Sakkwato.
A cewarsa, matakin komawa APC ya biyo bayan dogon nazari da tuntuba da magoya bayansa.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa dangantakar sa da magoya bayansa da jam’iyyar APC za ta kasance ne ta hannun shugaban ƙungiyar magoya bayansa, Farfesa Hamza Maishanu, tare da shugabannin jam’iyyar.
Bafarawa ya kuma jaddada cewa ya janye daga siyasar neman muƙami, yana mai cewa ba shi da sha’awar tsayawa takara a kowace kujera a nan gaba.
