
Akalla mutane 13 ne, ciki har da karmin yaro suka mutu sakamakon tsawa da ta fada wasu sassan ƙasar Bangladesh a ranar Lahadi.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake fama da ƙaruwar asarar rayuka sakamakon yanayin tsananin zafi da kuma tsawa a sassan ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na Anadolo ya ruwaito cewa, walƙiyar ta kashe mutane tara a gabashin yankin Brahmanbaria da kuma tsakiyar Kishoreganj.
Tun da farko, Hukumar Hasashen Yanayi ta Bangladesh (BMD) ta fitar da sanarwar cewa za a samu tsawa a wasu yankuna na ƙasar, a daidai lokacin da ake fuskantar matsanancin yanayin zafi.
A wani rahoto daga ranar 28 ga Afrilu, akalla mutane 17 sun rasa rayukansu a sassa bakwai na ƙasar sakamakon walƙiyar, lamarin da ya haifar da bukatar gaggawa na kiyaye rayuka da samar da tsaro.