Gwamnatin Jihar Yobe, ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana a jihar domin kare ɗalibai, biyo bayan taɓarɓarewar rashin tsaro a wasu jihohin ƙasar nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya fitar a jiya Asabar.
Ya bayyana cewa an yanke wannan mataki ne bayan taro kan sha’anin tsaro da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tare da hukumomin tsaro, inda suka yi nazari kan barazanar da makarantu ke fuskanta a jihar.
Sanarwar, wacce sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi, Dokta Bukar, ya sanya wa hannu, ta ce an rufe makarantun kwana nan take har sai al’amura sun daidaita.
Gwamna Mai mala Buni, ya roki jama’ar jihar da su ci gaba da yin addu’a domin samun zaman lafiya, inda kuma ya tabbatar da cewa gwamnati tana ɗaukar matakai don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan mataki na zuwa ne biyo bayan sace ɗalibai da ’yan bindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja.
