Gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe daukacin makarantun sakandiri na kwana na Unity Colleges guda 47 dake fadin kasar nan.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta tarayya, ta aikewa shugabannin makarantun sakandirin na kwana.
A cewar daraktan makarantun sakandirin Hajiya Binta Abdulkadir ta ma’aikatar ilimin, ta bayyana cewa an dauki wannan matakin ne biyo bayan sace daliban makarantun sakandirin jahohin Kebbi da kuma Neja a baya bayan nan.
- Gwamnatin tarayya ta lalata makomar ilimi a kasar nan-ASUU
- Matsalar Tsaro ta ragu da kashi 80 – Gwamnatin Tarayya
Sanarwar ta kuma bukaci shugabannin makarantun da abin ya shafa da su tabbatar sun bi wannan umarnin na rufe makarantun baki dayan su.
Makarantun sakandirin da wannan abun ya shafa sun hadar da Kano da Zariya da Daura da Sakkwato da Potiskum da dai sauran su.
