Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a birinin Alaska na Amurka a ranar 15 ga watan Agusta.
Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa ganawarsa da Putin gagaruma ce kuma za ta gudana ne a ranar Juma’a mai zuwa a Alaska.
Babu wani cikakken karin bayani kan ganawar a sanarwar ta Trump, amma dai ana ganin batun tsagaita wuta a yakin Rasha da Ukraine ne zai kasance maudu’i.
Tun da farko a ranar Alhamis, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tabbatar da shirin ganawa da Trump kan yaƙin Ukraine, inda ya ce ya na ganin Hadaddiyar Daular Larabawa ce za ta kasance mai masaukin manyan bakin biyu.
An shafe sama da shekara uku ana gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine kuma Trump ya sha nanata burinsa na kawo ƙarshen yakin cikin gaggawa.
