Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan wata takarda da ke ba da umarnin janyewar ƙasar daga wasu hukumomi na duniya guda 66.
Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa daga cikin hukumomin da abin ya shafa akwai 31 na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda gwamnatin ta bayyana cewa ayyukansu ba sa tafiya da muradun Amurka.
Sauran hukumomin MDD da ke cikin jerin sun haɗa da waɗanda ke kula da shirye-shiryen lafiyar iyali, lafiyar mata da yara, wanzar da zaman lafiya, da kuma yaƙi da cin zarafin mata a lokutan rikice-rikice.
Wasu daga cikinsu kuma na aiki ne kan batutuwan sauyin yanayi, ƙarfafa dimokuraɗiyya, da tabbatar da zaman lafiya a duniya.
