Majalisun dokokin kasar nan, sun amince da ƙudirin kasafin kuɗin ƙasa na shekarar 2025 na naira tiriliyan 54.99, a zamansu na ranar Alhamis.
Kasafin wanda ke ƙunshe da kuɗaɗen yau da kullum da manyan ayyuka da biyan bashi da kuma hasashen samun kuɗin da za a cike giɓin kasafin kuɗin kamar haka:
A ranar 5 ga watan Fabrairu ne shugaba Tinubu ya ƙara yawan kuɗin kasafin na 2025 daga naira tirirliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2,
Bisa dalilan samun ƙarin yawan kuɗaɗen shiga da hukumomi suka samar wa gwamnati.
Tinubu ya nemi majalisun su amince da ƙarin yawan kasafin a wasiƙu da ya aike wa majalisun guda biyu da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta.
Dama dai, tun a watan Disamban 2024 ne dai shugaba Bola Tinubu ya yi miƙa kasafin ga majalisun dokokin ƙasa.
