
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi na musamman a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, domin murnar cikar ƙasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kwamitin shirya bukukuwan Ranar ‘Yancin Kai a birnin tarayya Abuja.
Sanata Akume ya bayyana cewa Ranar ‘Yancin Kai na bana tana zuwa a lokaci mai muhimmanci, inda ya kamata a zauna a yi nazari kan ƙalubale da nasarori da Najeriya ta fuskanta tun daga 1960 zuwa yanzu.
Ya ce wannan lokaci ne da ya kamata al’ummar Najeriya su yi duba kan inda suka fito, inda suke, da kuma inda suke son zuwa a nan gaba.
A cewar jadawalin da aka fitar, bukukuwan za su fara ne da Taron Manema Labarai a ranar 25 ga watan Satumba, sai tarukan addini, ayyukan mata da matasa da kuma nune-nunen fasaha.
Bukukuwan za su ƙare da jawabin shugaban ƙasa da liyafar Ranar Yancin Kai a ranar 1 ga watan Oktoba.
A cikin wannan biki na musamman, gwamnati za ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken Nigeria@65 Compendium, wanda zai ƙunshi bayanai na musamman kan ci gaban ƙasa da aka samu cikin shekaru 65.